Gwammatin Tarayya ta bada Umarnin Sake Bude Makarantu

0
183

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin sake bude makarantu bayan shafe watanni suna kulle sakamakon bullar annobar COVID-19.

Dr. Sani Aliyu, Babban jami’in tsare-tsare na kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 ne ya bayar da umarnin sake bude makarantu a yau Alhamis.

Aliyu, Wanda ya umarce su dasu yi shirin da yakamata, yace sake bude makarantun zai kasance rukuni-rukuni.

“Dangane da makarantu wadanda suka hada Firamare, Sakandire, da manyan makarantu. Makarantu zasu fara shiri sake bude makarantu”, Inji shi.

“Haka kuma, muna bada umarni ga jihohi su tabbata anbi matakan da aka shimfida da kuma kirkirar matakan lura da su”.

Gwamnatin tarayya dai ta bada umarnin rufe makarantu a watan Maris don dakile yaduwar cutar Corona.

Sai dai a watan Yuli ne gwamnatin ta amince da sake bude makarantun Sakandire ga yan ajin karshe domin basu damar rubuta jarrabawar kammala Sakandire ta WAEC.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here