An Kashe Wani Mutum a Kano Bayan Zazzafan Musu a Teburin Mai Shayi

0
233

Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum mai suna Umar Abubakar ya rasa ransa bayan zazzafan musu a teburin mai shayi a unguwar Aisami dake karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Mamacin ya rasa ransa ne bayan wani mai suna Auwal Balarabe wanda ke hannun yan sanda yanzu haka ya daba masa wuka.

DSP Abdullahi Haruna, Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace mutumin ya mutu a asibitin Murtala bayan jami’an yan sanda sun kaishi asibitin.

Kiyawa yace kwamishinan yan sanda na jihar Kano ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin, inda za’a gurfanar da wanda ake zargin gaban kutu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here