Zan Bayar da Umarnin Kama Duk Dan Siyasar da yayi Batanci a gare ni – Gwamna Matawalle

0
134

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargadi yan hamayya na jami’iyyar APC da sauran jami’iyyu da su iya bakin su ko kuma su tsinci kansu a gidan Kaso.

Matawalle na fadin hakanne yayin jawabi ga dubban magoya bayan jami’iyyar APC da suka chanza sheka zuwa jami’iyyar PDP a jihar yau Laraba.

Gwamnan yace zai kama tare da gurfarnar da dukkan dan siyasar da ya bata masa suna.

Matawalle yace “Idan kasan baza ka iya kare abinda kace ba, abinda yafi ma sauki shine ka dena bata sunan mutane saboda zan bada umarnin kama duk wanda yake aikata hakan kuma sai yaje gidan Kaso.”

Gwamnan yayi bayanin cewa wasu yan siyasar na amfani da kalaman batanci don cimma burin su na siyasa saboda sun rasa hujja.

Ya gargadi irin wadannan yan siyasa da su kiyaye ko su fuskanci fushin hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here