TB Joshua Ya Gargadi Messi Kan Shirin Barin Barcelona

0
155

Mamallakin Majami’ar  Synagogue, Temitope Joshua, wanda aka fi kira da TB Joshua, ya gargadi dan wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona, Lionel Messi, kan barin Kungiyar.

Joshua yayi gargadin ne a shafinsa na Instagram a yau Laraba.

Inda ya rubuta “Ba shawara ce mai kyau ba ga Lionel Messi ya bar Barcelona. Ba abu ne mai yuwuwa ba ka kafa alaqa mai kwari da mutumin da ya bar alaqa a baya mai daci. Wannan shawara zuwa ga Messi”.

Dan Wasa Messi, wanda ya lashe gasar dan wasa mafi kwazo ta duniya har sau 6 ya nemi barin kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona bayan shan kashi da kungiyat tayi a hannun Bayern Munich da ci 8 da 2 a gasar zakarun nahiyar Turai.

Rahotanni dai sun bayyana cewa Messi na tattaunawa da Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, kungiyar da tsohon kocin Barcelona yake a matsayin Manaja a yanzu.

Sai dai, Barcelona taki yarda ta saki dan wasan nata inda ta jaddada cewa dole sai an biya Euro Miliyan 700 kafin ta bar Messi ya tafi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here