Ko an bude Makarantu Baza Mu Janye Yajin Aikin da Muke yi ba -ASUU

0
152

Kungiyar Malaman Jami’io’i ta Kasa(ASUU) a yau Laraba tace baza ta dawo harkokin koyarwa ba har sai anbiya bukatun ta wadanda suka sanya ta tsunduma yajin aiki kafin bullar annobar COVID-19.

Sannan kungiyar tace bata sukar kiran da ake yi na sake bude makarantu a kasarnan.

Haka kuma kungiyar ta buka ci yan Najeriya “Suyi alkalanci na gaskiya kan wannan matsaya”.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, Babban mai kula da shiyyar Ibadan na kungiyar ta ASUU, Farfesa Ade Adejumo yace ” Koda an bude jami’i’o a yau, yajin aikin da muke yi kan tilastawa gwamnati ta cika alkawarin yarjejeniyar da muka yi da ita zai cigaba.

“Hakki ne akan mu mu janyo hankalin gwamnati kan ayyukan da suke kanta ga kasa da kuma yan kasa, haka muka yi kuma babu gudu ba ja da baya.

Shiyyar Kungiyar ASUU ta Ibadan dai ta hada da Jami’ar Ibadan(UI), Jami’ar Ilorin(Unilorin), Jami’ar jihar Osun(Unisun), Jami’ar jihar Kwara(Kwasu), da jami’ar kimiyya da fasaha ta Akintola(LAUTECH).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here