Jihar Kogi ta bi Sahun Osun da Legas Wajen Sanar da Ranar Komawa Makarantu

0
224

Gwamnatin jihar Kogi ta sanar da ranar 14 ga watan Satumba a matsayin ranar sake bude makarantun a jihar.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Mista Wemi Jones wanda yayi sanarwar a garin Lokoja yau Talata, yace gwamantin jihar ta yanke shawarar sake bude makarantun ne bayan jerin tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da duba irin shirin da makarantun gwamnati dana masu zaman kansu suka yi na tsare dalibai daga kamuwa da cutar COVID-19.

“Idan zaku tuna, Mai Girma Gwamna ya umarci a rufe dukkan Makarantu daga Firamare har zuwa Manyan makarantun gaba da Sakandire a jihar a ranar 23 ga watan Maris saboda bullar annobar COVID-19.

“Saboda haka, bayan tattaunawar da aka yi da masu ruwa da tsaki, Gwamnan jihar Kogi ya bada umarnin cewa dukkan makarantu zasu koma karatu a ranar 14 ga watan Satumba”, Inji Kwamishinan.

Sannan ya shawarci dukkan shugabannin makarantu su tabbata anbi ka’idojin kariya daga cutat COVID-19 wanda kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da annobar ya tsara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here