Gwamnatin Tarayya zata Kashe Sama da Tiriliyan 2 Wajen Samar da Wutar Lantarki ga Mazauna Karkara

0
127

Gwamnatin tarayya tace tana shirin samar da hasken wutar lantarki ga mazauna karkara wanda aikin zai lakume kudi Triliyan 2.3 karkashin shirin bunkasa tattalin arziki na ESP, wanda ofishin mataimakin shugaban kasa yake kula da shi.

Goddy Jedy-Agba, karamin Ministan wutar lantarki ne ya bayyana hakan a Abuja a yau Talata, yayin kaddamar da aikin samar da wuta mai karfin Kilo mita 12 ta hasken lantarki a cibiyar matakin lafiya ta farko dake Karu wanda kamfanin Volus Energy Ltd ya samar.

Mista Jedy-Agba yace aikin zai samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga gidaje Miliyan 5 a yankin karkara a Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa aikin samar da wutar lantarkin ga mazauna kankara zai kara karfin gwiwa ga mutanen dake rayuwa a kauyuka da birane wajen sanya su fara kananan sana’o’i sannan su koma harkokin aikin noma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here