Babu Dalibin Da zai Koma Makaranta Sai An Saki Dadiyata – Sen. Dambatta

0
816

Shugaban kungiyar cigaban daliban Africa Sen. Mukhtar Sagir Dambatta ya umarci dukkanin daliban wannan kasa da su kauracewa komawa makaranta saboda batan wani malamin makaranta mai suna Abubakar Idris (Dadiyata)

Dambatta ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na twitter @chaliepher a yau 01/09/2020

Shugaban ya kara da cewa “wannan kasa tamu cike take da azzalumai da kuma wayanda basu san darajar dan adam ba”

“Abubakar Idris wanda aka fi sani da sunan (Dadiyata) Dan Najeriya ne kuma malamin makaranta ne wanda kuma yana da iyali an dauke shi wajen shekara daya babu labarinsa”

“A matsayin mu na wakilan alumma dole mu nuna fushinmu akan batan dadiyata saboda malami ne kuma mun dauki malamin makaranta uban kowa”

Dambatta yayi bayanin cewa ya tattauna da kungiyoyin dalibai daga sassa daban daban na wannan kasa kafin yanke wannan hukunci

Sen. Dambatta ya kara da cewa “Ina kira da dalibai da suyi hakuri da wannan hukuncin da muka yanke, mun yanke hakan ne saboda wannan alamari zai iya faruwa da kowanne dalibi ko kuma malami a wannan kasa mu kuma bamu yarda aci zarafin kowanne dan kasa ba”

“Ina gargadin gwamnan Kaduna da ya saurara da cin zarafin mutanen da yake haka idan kuma ba haka ba zai fuskanci fushin mu”

Daga karshe Sen. Mukhtar Sagir Dambatta ya yayiwa wannan kasa adduar fatan alkhairi da kuma adduar kare wanna n kasa daga hannun masu san tarwatsa alumma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here