An Fara Bayar da Hayar Shadda Getzner A Kano

0
5758

Jaridar Kano Focus ta rawaito labarin cewa wani Taila a unguwar Tal’udu cikin birnin Kano, mai suna Ibrahim Bature Yakubu ya bude wajen bayar da hayar kayan sawa a jihar.

Malam Yakubu ya shaidawa Jaridar Kano Focus cewa ya karbi kira na mutane sama da 300 cikin sati daya da fara kasuwancin nasa a ranar 24 ga watan Agusta.

Tailon yace ya himmatu wajen fara bayar da hayar kaya ne don bukatar samarin dake son sababbin kaya wanda zasu sanya wajen halartar Bukukuwa da sauran taruka.

“Na lura da cewa yana yin tsada ga mutane su su maallaki Kaya, sai na yanke shawarar siyan kayan, tare da dinkawa.

“Muna bada aron Atamfa ta mata akan Naira 1500, haka muke bayar da shadda ta maza, amma muna bayar da hayar Getzner akan kudi Naira Dubu 3.

” Lokacin hayar yana faraqa daga 9 na safe zuwa 10 na yamma”, Inji shi.

Yakubu yave ya fara kasuwancin ne da Naira 30, 000 amma wasu mutane sun bayyana aniyar au na zuba hannun jari.

Sannan ya kara da cewa iyayen sa sun yi tunanin ya rasa hankalinsa bisa tunanin fara irin wannan sana’ar amma yana da kwarin gwiwar cewa yana samar da abu mai kima ga al’umma.

Sannan yayi kira ga matasa su kasance masu neman na kansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here