Tsarin Yadda Daliban Jami’ar Jihar Legas Zasu Koma Makaranta

0
146

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa daliban manyan makarantu a jihar zasu koma harkokin karatu ne cikin tsarin rukuni-rukuni.

Mataimakin shugaban jami’ar jihar Legas, farfesa Olanrewaju Fagbohun, ne ya sanar da hakan a yau Litinin.

Idan za’a iya tunawa dai, Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, a ranar Asabar ya sanar da cewa manyan makarantun gaba da sakandire za’a basu damar komawa karatu daga ranar 14 ga watan Satumba, yayin da makarantun firamare da Sakandire zasu dawo karatu ranar 21 ga watan Satumba.

Mista Fagbohun, yayin da yake amsa tambayoyi a wani shirin gidan Rediyon EKo 89.7 FM, yayi bayanin cewa daliban da suke a mataki na 4 da na 5 da mataki na 6 sune zasu fara komawa makaranta kafin ragowar.

Mataimakin shugaban jami’ar yayi bayanin cewa malaman jami’i’a zasu dinga zama daga karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na rana.

Sannan ya bayyana cewa daliban da suke mataki na 2 dana 3 zasu dawo makaranta wata 2 kafin su fara jarrabawa.

“Bayan dawowar daliban dake mataki na 4 da na 6, daliban dake mataki na 2 dana 3 zasu dawo karatu wata biyu kafin su fara jarrabawa.

” Dawowar Daliban dake mataki na 2 dana 3 an raba shi zuwa kwanaki daban-daban na cikin mako.

A duk ranakun Litinin da Laraba, daliban dake mataki na 3 zasu kansance a makaranta. A duk ranakun Talata da Alhamis, daliban dake mataki 2 zasu kansance a makaranta. An dauki matakin hakanne domin tabbatar da an bada tazara kuma an tsare lafiyar dalibai da ma’aikatan jami’ar.

“Kamar yadda hukumar NCDC ta nemi a samar da wajen kula da lafiya, Jami’ar LASU tana da tawagar dake yaki da cutar COVID-19 wadanda zasu tabbatar da abin ka’idojin da aka shimfida.

” An tanadi guraren killacewa a cikin jami’a, jami’ar Lasu ta shirya kula da dalibai da masu kawo ziyara”.

Sannan yace jami’ar ta kammala jarrabawa ta kafar sadarwa ga daliban dake karatun digirin digir-gir.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here