Sarkin Karaye Ya Jajantawa Wadanda Iftila’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa a Garin Rogo

0
156

Sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II ya jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Garin Madaki dake Karamar hukumar Rogo.

Sarkin ya bayyana jajantawar sa ne yayin da yake karbar rahoto kan lamarin daga hakimin Rogo, Wamban Karaye Alhaji Muhammad Muhammad Mahraz Karaye a Fagaci Fadar Sarkin Karaye.

Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II ya bukaci wanda abin ya shafa su dauke shi a matsayin kaddara ta Ubangiji. Sannan yayi addu’a ga wadanda suka rasa ransu tare da addu’ar samun lafiya ga wadanda suka jikkata.

Sarkin ya yabawa gwamnatin jihar Kano da dukkan wadanda suka bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Rahoton da Hakimin Rogon, Alhaji Muhammad Maharaz ya gabatar ya bayyana cewa an samu ambaliyar ruwan ne sakamakon saukar ruwan sama mai karfin gaske a ranar 22 ga watan Agusta, wanda ya kai ga rasa rayukan mutum 2 da jikkata mutane da dama tare da rushewar gidaje.

A wani bangaren kuma, Sarkin Karaye, ya yaba da yadda ake samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar masarautar.

Sarkin yayi yabon ne yayin da yake karbar rahoton tsaro na watan Mayu, Yuni, Yuli da Agusta daga Hakiman Rogo da Karaye.

Sannan Sarkin yayi umarnin a aikta takardar godiya ga kamfanin BUA bisa tallafin da suke bawa al’ummar Masarautar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here