Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta Zargin cewa Tana da hannu Kan Batan Dadiyata

0
190

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta cewa tana da hannu kan sace Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

Wasu mutane da ba’a san ko su waye ba ne dai suka sace Dadiya shekara daya data wuce. An sace shi ne a gidansa dake Barnawa kusa da cikin garin Kaduna.

Yan sanda a jihar sun ce yana dawowa gida da misalin karfe 1 na dare a lokacin da yan bindigar suka sace shi a cikin motar sa BMW.

Tun bayan shekarda guda da bacewar tasa har zuwa yau ba’a samu labarin sa ba ko motar tasa.

A wata sanarwa da kwamishinan shari’a ta jihar Kaduna, Aisha Dikko ta fitar a yau Litinin tace gwammatin jihar bata da masaniya kan inda Dadiyata yake.

“Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kaduna ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna bata da masaniya kan inda Abubakar Dadiyata yake kuma bata da hannu kan sace shi”. Inji ta.

Abubakar Idris wanda ake kira dadiyata yana amfani da shafukan sadarwa na zamani wanda aka san shi wajen sukar gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ma’aikatar shari’ar ta jihar Kaduna ta kuma ce Gwamnatin jihar bata taba kai karar Dadiyata ga jami’an tsaro ba kuma bata taba shigar da kara kan sa ba a gaban kotu.

Dadiyata wanda mabiyin darikar Kwankwasiyya ne, ansha jin Jagoran kungiyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yin kira ga hukumomin tsaro su nemo inda yake.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here