‘Daga Qasidar Yabo na Koma Wakokin Hausa’ – Mawaki M Mars

0
311

Matashin mawakin Hausa mai suna Mukhtar Isah Usman wanda akafi sani da M Mars ya bayyana cewa tun tasowarsa yake sha’awar shiga fannin rera waka inda yace tun daga makarantar Islamiyya ya fara rera Qasidar yabo wanda ya kaishi ga komawa fannin rera wakokin Hausa.

M Mars, Wanda an haife shi ne a unguwar Na’ibawa dake Karamar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano ya bayyana hakanne yayin tattaunawa da Jaridar PRIME TIME NEWS a yammacin jiya Lahadi a Kano.

“Gaskiya ni tunda na taso, ina son harkar waka amma qasida nake yi ko a makarantun mu idan za’a je ziyara ta Maulidi nine nake rubuta wasika, sannan akwai abokina mawaki yana harkar waka shima shine ya kara jan hankalina na shiga harkar waka” Cewar Mawaki M Mars.

Mawakin yace ya samo asalin inkiyar ‘Mars’ ne daga wani group din su mai suna Mars, kuma wakar Mars ce wakarsa ta farko da ya fara fitarwa.

“Lokacin da muka bude group din, sai muka ga wane suna yakamata a bashi, sai kowa ya kawo nashi aka harhada aka tashi ‘MARS’ ni kuma aka bani shugaban group din, daga nan ko ina na wuce sai adinga kirana ‘Mai MARS’ toh anan M Mars ta samo Asali”.

Sannan mawakin yace da farko ya fara wakokin Gambara na Hausa ne(Hip-pop) amma yanzu yafi karkata zuwa wakokin ‘Nanaye’.

Sannan ya bayyana cewa yafi kaunar wakar ‘Halima’ cikin wakokinsa kuma itace wacce masoyansa suka fi so.

Mawakin yace ” Wakar Halima ta kunshi soyayya, da yadda za’a zauna har ta kai ga Aure ma wakar ta kunsa.

“Akwai wata babbar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood mai suna Halima Atete, saboda yinta da nake yi naga yakamata na bawa sunan wannan wakar ta Halima.

Mawakin ya kara da cewa ya fuskanci qalubale da dama amma kasancewar nasororin da ya samu a yanzu bazai iya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta ba.

Sannan yace ya shirya tsaf don faranta ran masoyansa ta hanyar sakin wata sabuwar wakarsa mai suna “Sirrin Zuciya”.

Daga karshe yayi fatan Alkhairi ga masoyan sa inda ya nemi su kara masa karfin gwiwa sannan yayi kira ga sauran mawaka su kara hada kansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here