Baza mu kara wa’adin da Muka Sanya na Kammala Rijista ba -NECO

0
170

Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta kasa(NECO) ta sanar da cewa baza ta kara wa’adin da ta sanya na kammala yin rijistar jarrabawar kammala Sakandire ta kasa ba a ranar 10 ga watan Satumba.

Ma’aikatar ilimi ta kasa ce ta amince da wa’adin na ranar 10 ga watan Satumba, sannan hukumar ta NECO tace akwai isasshen lokaci na yin shiri yayin da jarrabawar ke karatowa.

A wata sanarwa da magatakarda kuma babban jami’in hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta kasa(NECO), Farfesa Godswill Obioma, ya fitar a yau Litinin a Abuja, ta bayyyana cewa za’a fara jarrabawar kammala Sakandire ta shekarar 2020 a ranar 5 ga watan Oktoba sannan a kammala ranar 18 ga watan Nuwamba.

Yace, “Hukumar shirya jarrabawar Kammala Sakandire ta kasa na farin cikin tunatarwa masu ruwa da tsaki da sauran al’umma cewa wa’adin da aka sanya na yin rijistar jarrabawar kammala Sakandire ta shekarar 2020 zai kare ranar Alhamis 10 ga watan Satumba.

” Ba wani dalili da zai sa a kara wa’adin kamar yadda ma’aikatar ilimi ta kasa ta amince. Hakan anyi shine don bayar damar yin shirin da yakamata na gudanar da jarrabawar.

“NECO na tunatar da masu ruwa da tsaki da al’umma gabadaya cewa jarrabawar kammala Sakandire ta kasa ta shekarar 2020 za’a fara ta ne a ranar 5 ga watan Oktoba kuma a kammala ranar 18 ga watan Nuwamba.

” Sannan muna amfani da wannan dama wajen sanarwa da masu ruwa da tsaki cewa za’a saki jadawalin lokaci da ranakun gudanar da jarrabawar nan bada jimawa ba”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here