Gwamnatin Jihar Kano Zata Gina Makarantun Sakandire 130 a Kananan Hukumomi 24 dake Jihar

0
168

Gwamnatin jihar Kano tace ta ware Naira Miliyan 880 don gyara makarantar gaba da Firamare guda daya a kowacce karamar hukuma a kananan hukumomi 44 dake jihar.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Sanusi Kiru wanda ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin manema labarai yau Lahadi, ya kara da cewa shirye-shirye sun kammala wajen samar da karin makarantun Sakandire na yan mata guda 130 a jihar.

Alhji Sanusi Kiru yace makarantun za’a kafa su ne a wasu kananan hukumomi 24 da aka zaba, inda ya kara da cewa aikin zai hadar da samar kananan Sakandire 75 da manyan makarantun Sakandire 55.

Sannan yace matakin na daga cikin kokarin da ake na bunkasa ilimin mata a jihar.

Kwamishinan yace “Gwamnatin jiha tare da hadin gwiwar bankin duniya zasu gyara sauran makarantu don inganta ilimin mata da kananan yara.

” Haka kuma gwamnatin jiha ta ware Kudi Miliyan 880 don gyara makarantar Sakandire daya a kowacce karamar hukuma”.

Sannan yace jihar zata bayar da Miliyan 20 ga kowacce karamar hukumar domin gyara makarantu.

Sanusi kira yayi bayanin cewa an kafa kwamitin da ya hada da dattijan cikin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar aiwatar da aikin.

Kwamishinan ya kuma ce jihar ta samu nasara a jarrabawar kammala Sakandire ta WAEC da ake yi, sannan ba a samu mai dauke da cutar COVID-19 ba cikin dalibai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here