Gwamnan Jihar Zamfara Zai Samar da Dokar Yin Hukuncin Kisa Ga Masu Tukin Ganganci a Jihar

0
154

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi alkawarin daukar tsattsauran mataki na hukuncin kisa ga masu tukin ganganci a jihar bayan hadarin da ya lakume rayukan mutane 16 a yammacin Larabar da ta gabata.

Hadarin ya faru ne yayin da wata babbar mota ta kubce tare da afkawa kan motoci guda 4 wadanda suke dauke da magoya bayan gwamnan a titin Gusau zuwa Funtua.

Gwamman ya bayyana hakanne yayin da ya jagoranci mukarabban gwamnatin sa da mahukuntan kamfanin BUA zuwa ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, a ranar Asabar.

Gwamnan ya sanar da bayar da tallafin Naira Miliyan 2 ga iyalin kowanne mamaci, wanda ke da mata da Naira Miliyan daya daya da dubu dari 5 ga marasa Aure.

Sannan ya sanar da cewa zai sanya magadan kowanne daya daga cikin mamatan kan tsarin biyan alawus na Naira dubu 50 duk wata.

Haka kuma yayi karin bayanin cewa gwamnatin sa zata sanya na’urar rage gudu a manyan tititunan jihar da ta rage nauyin manyan motoci tare da yin gwajin shan miyangun kwayoyi ga matuka ababan hawa don kaucewa tukin ganganci wanda ke jawo asarar rayuka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here