
Babban Sufeto Janar na Yan Sanda na kasa, Mohammed Adamu, ya umarci kwanishinonin yan sanda na jihohin Edo da Ondo su kara shiri a yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnoni a jihohin.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta kasa, Frank Mba ne ya sanar da hakan a yau Lahadi a Abuja.
Mista Mba yace babban Sufeton yan sandan ya bayar da umarnin ne bayan ya karbi rahoto daga kwamishinonin yan sandan jihohin adai-dai lokacin da ake shirin gudanar da zabe a ranakun 19 ga watan Satumba a jihar Edo da 10 ga watan Oktoba a jihar Ondo.
Yace rahoton ya bankado cewa, amfani da yan daba da yan siyasa suka yi yayin tallan yan takara, ka iya sa a samu rigima tsakanin su.
Sannan ya kara da cewa babban sufeton ya gargadi yan siyasa da magobayan su a jihohin guda biyu, akan su bi doka da oda.