Gwamnatin Jihar Legas ta Sanar da Ranar Komawa Manyan Makarantu a Jihar

0
220

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ya bada umarnin sake bude manyan makarantu a jihar daga ranar 14 ga watan Satumba.

Gwamnan ya sanar da hakanne yayin yiwa manema labarai jawabi a gidan gwanatin jihar.

“Ina mai farin cikin sanar da cewa za’a bawa manyan makarantun mu damar sake budewa daga ranar 14 ga watan Satumba”, inji shi.

Idan za’a iya tunawa dai tun a watan Maris, gwamnatin tarayya ta sanar da rufe makarantu don dakile yaduwar annobar Corona.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here