Gwamnatin Jihar Kaduna ta Hana Babura Masu Kafa Uku Yin Aiki a Manyan Tititunan Birnin Jihar

0
189

Gwamnatin jihar Kaduna ta hana matukan babura masu kafa uku bin manyan hanyoyin jihar na cikin gari a cigaba da gyare-gyaren da akewa tsarin sufuri a jihar.

Aisha Sa’idu Bala, Babbar Darakta a hukumar kula da sufuri ta jihar Kaduna(KADSTRA), ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a Kaduna.

Inda tace “Dukkan Babura masu kafa uku, ” Keke”, an dakatar da su daga yin aiki a titin Kawo zuwa Ali Akili, Ahamdu Bello Command Junction daga ranar 31 ga watan Agusta.

Sannan tace hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kaduna zata tabbatar da anbi sabuwar dokar.

Aisha Sa’adu Bala tace gwamnatin jihar ta samar da sabbin dokoki ga masu sana’ar tuka ababan hawa a jihar.

Hakanan ta kara da cewa, hukumar ta KADSTRA ta fara rijistar babura masu kafa uku a watan Yuli sannan za’a kammala rijistar a karshen watan Satumba.

Ta kuma shawarci masu ababan hawa su tabbata sun yi rijistar gudanar da harkokin su.

Wasu daga cikin matuka baburan mai kafa uku sun shaidawa kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) cewa sabuwar doka zata shafi hanyoyin da suke samun kudin da suke gudanar da rayuwar su ta yau da kullum.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here