An Saki Wata Sabuwar Waka Daza ta Taimakawa Dalibai Wajen Iya Ilimin Lissafi(Mathematics)

0
201

Jami’ar Ibadan(UI) ta kaddamar da wata waka wacce aka yi ta don saukakawa dalibai yadda zasu iya gane ilimin lissafi(Mathematics). Wakar anyi mata suna ‘Wakar mafita ga ilimin lissafi'(MATMUSIC).

Akin Salami daga sashin ilimin kananan yara na jami’ar ne ya yayi wakar.

Mataimakin shugaban jami’ar, Idowu Olayinka, ne ya shaida kaddamar da wakar a ranar juma’a a garin Ibadan.

Yayin da yake jawabi kan amfani da wakoki wajen saukaka iya ilimin lissafi, Mista Olayinka yayi bayanin cewa dole ne a dinga amfani da abubuwan kirkira na fasaha domin bunkasa koyarwa.

Sannan ya kalubalanci masu bincike akan su gano sabbin hanyoyi na bunkasa hanyar koyo da koyarwa don mayar da fannin koyarwa abin sha’awa wanda zai samar da kyakkyawan sakamako.

“Na yarda akwai damarmaki na koyar da ilimin likitanci ta hanyar waka, mayar da koyarwa abar sha’awa ga masu koyo da kokarin likita, mai bada umarni, malami, hakan zai mayar da koyarwa abu mai kyau.”

Mista Salami yayin da yake jawabi yace dabarar samar da wakar MATMUSIC na daga cikin gogewar da ya samu a makarantar ma’aikatan jami’ar, inda ya koyar da ilimin lissafi sanan ya gano cewa dalibai na son ilimin yayin da ya samar da da waka.

Sannan yace wakar yayi ta ne tare da dalibai kuma an samar da ita ne don saukakawa dalibai su iya tare da fitar da matsala a Math a makarantun Firamare.

Haka kuma yace an mikawa makarantu 20 wakar dake jihar Oyo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here