“A wajena Kano da Ilorin Duk Abu Daya ne” – Sarkin Kano

0
436

Gwamnan jihar Kwara, Abdrahaman AbdulRazaq a jiya Juma’a yace masarautun gargajiya nada rawar takawa wajen cigaba da samun zaman lafiyar al’umma kuma suna da matukar muhimmanci wajen samun kwanciyar hankali.

AbdulRazaq na magana ne a garin Ilorin, babban birnin jihar, yayin da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya kai masa ziyara.

“A matsayin mu na gwammati muna mutukar girmamam masarautun gargajiya. Duk da turakan gwammati guda uku ne, na yarda masarautun gargajiya ne cikon na hudu. Shiyasa lokacin mulkin sojoji suka mayarda masarutun cewa zasu dinga karbar kudaden su kaitsaye daga kananan hukumomi”. Inji Gwamnan.

Gwamnan ya kuma yabawa dangantakar dake tsakanin masarautar Kano da ta Ilorin, da kuma alaqar kasuwanci da noma dake tsakanin jihohin.

Aminu Ado Bayero,Wanda mahaifiyarsa yar asalin garin Ilorin ce yace yazo garin ne domin samun albarka daga dangin mahaifiyarsa.

Sannan yayi ta’aziyya ga gwamnan bisa rasuwar mahaifin sa, inda yayi addu’ar Allah ya jikan sa.

“Dalilin ziyarata shine na dawo gida, inda yake asalina, a wajena Kano da Ilori duk abu daya ne. Nan ne gidana a bangare mahaifiya, ina farinciki kasancewa anan, ba wannanne karon farko da nazo nan ba”.

“Amma wannan karon shine zuwa na musamman saboda shine farkon zuwana bayan na samu sarauta, na godewa Allah bisa wannan.” Inji Sarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here