Matasan Arewa Sun Nemi A Rufe Shafukan Batsa a Kafafen Sadarwa na Najeriya

0
466

Kungiyar matasan Arewacin Najeriya ta Arewa Youth Consultative Council, tayi kira ga ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed da ya rufe dukkan shafukan batsa a kafofin sadarwa na Najeriya.

A wata wasika da aka aikawa ministan mai dauke da kwanan wata 27 ga watan Agusta kuma mai dauke da sa hannun Muhammad Ibrahim Milb, babban jami’in kula da sadarwa na kungiyar,kungiyar ta nemi sanya hannun ministan cikin gaggawa don toshe shafukan batsa dana dabi’un da basu kamata ba a Najeriya domin dakatar da munanan dabi’u tsakanin matasa.

Wasikar wacce aka aikowa Jaridar PRIME TIME NEWS da Kwafinta tace matakin yin kira ga ministan an dauke shi ne a taron da kungiyar ta gudanar ta kafar sadarwar Zoom mai taken “Tasiri da Kalubalen fasahar zamani ga matasan Arewa”.

Hakanan wasikar ta nemi ministan ya sanya kula da kuma wani shiri da zai dinga cire dukkan wasu bayanai ko wata hanya da zata kai ga matasa shiga shafukan batsa.

Kungiyar tace dukkan wasu dai-daikun mutane ko kamfanunuwa da suka ki bin tsarin za’a hukunta su tare da cin tarar su.

Sannan kungiyar tayi bayanin cewa taron nata ya samu halartar shugabanninta na shiyoyi, matasa da kuma mambobinta na jihohin Arewa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here