Jami’ar Azman Dake Kano Zata Fara Gudanar da Harkokin Koyarwa

0
324

Mataimakin shugaban jami’ar kimiyyya da fasa ta Kano dake garin Wudil, Farfesa Shehu Alhji Musa a jiya Alhamis ya bayyana cewa a shirye yake wajen bada horo don gogewa da goyon baya ga jami’ar Azman dake Kano.

Jami’ar Azman babbar makaranta ce a Kano da zata fara gudanar da harkokin koyarwa nan bada jimawa ba sannan itace jami’a ta farko ga yan asalin jihar wacce take mallakin shugaban rukunin kamfanin Azman, Alhaji Dr. Abdul-Manaf Sarina.

Farfesa Shehu yace yaji dadin irin kokarin da Dr. Sarina keyi wajen bunkasa bangaren ilimi a jihar Kano, inda yace hakan zai amfani dukkan yan Najeriya.

Mataimakin shugaban jami’ar ta KUST Wudil na fadin haka ne yayin da yake karbar bakuncin kwamitin tsare-tsare da aiwatarwa na jami’ar Azman karkashin jagorancin Farfesa Isa Dandago a ofishin sa.

Inda yace a shirye yake wajen bawa jami’ar Azman hadin kan da ake bukata.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Isa Damdago yace ziyarar tasu na dagacikin ayyukan kwamitin kafa jami’ar Azman na neman hadin gwiwa, aiki tare tare da gogayyya da sauran jami’i’on dake kasarnan.

Sannan ya bayyana cewa jami’ar zata fara harkokin karatu daga shekara mai zuwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here