Fitattun Yan Siyasa 11 da Matasan Kabilar Igbo Ke Son Su Nemi Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2023

0
206

Kungiyar Igbo For President Solidarity, IPSC, ta fitar da fitattun mutane 11 daga yankin kudu maso gabashin kasarnan da suka chan-Chanci yin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Shugaban kungiyar, Dr. Olukayode Oshiariyo, ne ya sanar da sunayen Bayan taron da kungiyar tayi a Abuja yau Juma’a, inda kungiyar tace yanzu lokaci ne da kasarnan zata samar da shugaban kasa dan kabilar Igbo.

“Kungiyar IPSC ta yanke shawarar cewa dan kabilar Igbo ne zai zama shugaban Najeriya a zaben shekarar 2023.

” Zamu cigaba da yin tuntuba a dukkan yankuna 6 na kasarnan, zamu ziyarci Sarakuna don tattaunawa tare da tantance halayya da nagarta mutane 11 da muka fitar” Inji shi.

Mutanen da kungiyar ta fitar sun hada da: Dr. Ogbonaya Onu; tsohon gwamna Peter Obi na Anambra, Dr.Chiris Ngige, Sanata Rochas Okorocha; na jihar Imo, David Umahi na Ebonyi, Sanata Orji Uzor Kalu, Sanata Ike Ekweremadu, Sanata Enyinnaya Abaribe, Gwamna Ifeanyi Uba da Farfesa Kingsley Moghalu.

“Tun shekarar 1999 yankin kudu maso yamma, Arewa maso yamma da Kudu maso Kudu sun samar da Shugabannin kasa”.

“Saboda haka, a shekarar 2023, yankin da yafi dacewa ayi la’akari dashi shine yankin kudu maso gabas a matsayin yankin kudancin kasarnan da har yanzu bai samar da shugaban kasa ba”, cewar Mista Oshiariyo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here