An Umarci Yan Jarida Su Kauracewa Taron Manema Labarai da Fani Kayode Ya Shirya

0
122

Kungiyar yan Jaridu ta kasa reshen jihar Akwa Ibom ta yanke shawarar kauracewa taron manema labarai da tsohon ministn jiragen sama, Femi Fani Kayode ya shirya a jihar.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau juma’a, ta umarci dukkan wani dan Jarida kar ya halarci duk wani taro da Fani Kayode ya shirya.

Fani Kayode dai yasha suka bayan yaci mutuncin dan jarida Eyo Charles a wani taron manema labarai a Calabar, jihar Cross River.

Dan jaridar dai ya tambayi Fani Kayode ne kan wanda yake daukar nauyin ziyarar da yake kaiwa jihohi.

Sai dai tsohon ministan cikin fushi ya mayar da martani tare da kiran dan jaridar “Shashasha”.

Sai dai Fani Kayode ya nemi afuwa kan abinda ya aikata.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here