Yadda Kungiyar Boko Haram Ta Kashe Dattawan Jihar Barno 75 a Dare Daya – Ndume

0
228

Sanata mai wakiltar kudancin Barno, Ali Ndume, yayi bayanin yadda kungiyar Boko Haram ta hallaka dattawan garin Gwoza 75 cikin dare daya.

Ndume ya bayyana hakanne a jiya Laraba yayin tattaunawar masu ruwa da tsaki wanda kwamitin majalisar dattijai kan ayyuka na musamman da hukumar cigaban yankin arewa maso gabas ya shirya a Maduguri.

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan, wanda kuma daya ne daga cikin yan kwamitin, ya shaidawa mahalarta taron cewa kalubalen da mutanen Barno suke fuskanta bazai fadu ba.

“Idan kwamitin majalisar dattijai zai samu lokaci lokacin zaman su su zagaya wasu sansanoni ko da kusa da karamar hukumar Konduga ne, dukkan mu zamu fi fahimtar abinda mutane suke fuskanta”, inji shi.

“Ko ni din nan da nake Sanata, bazan iya zuwa garin Gwoza ba, mahaifata, saboda babu tsaro”. Inji shi.

” Jami’an tsaron mu suna iya kokarin su, kuma yakamata mu fada, amma yanayin ya kazanta. Mutane suna mutuwa a kodayaushe, ko dai a kai musu hari ko yunwa ta kashe su. Mun rasa rayuka dayawa.

“Akwai wani lokaci a garina Gwoza, dattawa 75 wadanda yawancin su na san su, yan kungiyar Boko Haram sun kai su wajen yanka dabbobi na garin suka yanka su kamar dabbobi.
Mutane biyu ne kadai suka tsira saboda jinin wadansu ya rufe jikin su, masu kisan sun yi zaton suma sun mutu.

“A dai garin Gwoza din, Boko Haram wata rana sun taba jera matasa maza suka bindige su”.

Sanata Ndume ya kuma yi kukan matsalar yunwa a jihar inda yace lamarin zai yi muni tunda babu kungiyoyin dake bada tallafi a Barno.

” Bamu san ina muka nufa ba ko bamu san mai zai faru ba damu a jihar Barno, tunda babu kungiyoyi masu zaman kansu dake bada tallafi”. Inji shi.

“Mutane suna mutuwa kullum anan, ina tabbatar muku cewa ko a yau da yammacin nan yunwa ta kashe wasu. Ba ina magana akan yara ba ina nufin manyan mutane.

Sannan yace wadanda matsaloli da saura da yawa ne suka ja hankalin sa wajen bukatar ganin an kafa hukumar cigaban yankin arewa maso gabas.

“Shawarata ce tasa aka kafa hukumar cigaban yankin arewa maso gabas, sannan na tabbatar da samuwar ta ne ba don komai ba sai dai don ganin an taimaki mutane sun fita daga wannan mummunan hali. Komai yana tafiya yadda ya kamata, muna jin dadi da irin ayyukan da suke yi.

“Sai dai abin bakin cikin, adadin kudin da ake warewa hukumar yayi kadan ya shawo kan matsalar da mutane suke fuskanta a jihar Barno kadai”. Inji shi.

Kwamitin majalisar dattawa dai karkashin jagorancin Yusif Abubakar, na ziyara a jihar Barno domin duba irin kokarin hukumar bunkasa yankin arewa maso gabas da hukumar bayar da agaji ta NEMA.

Ana saran Kwamitin zai ziyarci sansanin yan gudun hijira da sauran guraren da hukumar raya yankin arewa maaso gabas ta gudanar da ayyukan ta.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here