Sojoji Sun Saki Tsohon Shugaban Kasar Mali

0
130

Sojojin dake mulki a kasar Mali sun ce sun saki tsohon shugaban kasar, Boubacar Keita, wanda aka tsare tunda aka yi juyin mulki a kasar a ranar 18 ga watan Agusta.

Sojin junta, wadanda suka kira kan su kwamitin yantar da mutane na kasa(CNSP), sun ce sun sanarwa da mutane da kungiyoyin duniya cewa sun saki tsohon shugaban kasar, sannan yanzu haka yana masaukin sa.

Sakin Keita na daga cikin manyan bukatun kasashen dake makotaka da kasar Mali da kuma kungiyoyin kasashen ketare.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here