Sarkin Kano na Ziyara a garin Ilorin Dangin Mahaifiyarsa

0
305

Sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda mahaifiyarsa yar asalin garin Ilorin ce zai sauka yau Alhamis a jihar Kwara a ziyarar aiki da yake yi.

Idan za’a iya tunawa dai Alhaji Aminu Ado Bayero ya maye gurbin tsohon gwamnan babban banki na kasa(CBN) Sanusi Lamido Sanusi,wanda Gwamnan Kano Ganduje ya tube daga Sarauta.

Gwamnatin jihar Kwara tayi kira ga al’ummar jihar da su fito domin tarbar Sarkin Kanon.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan sadarwa, Harriet Afolabi ta fitar a safiyar yau Alhamis.

Sanarwar ta bukaci mazauna jihar Kwara da su lura da matakan kariya daga cutar CJOVID-19 da hukumar NCDC ta shimfida.

“Gwmanatin jiha tana matukar farin ciki tare da girmamawa ga zuwan Sarkin Kano, sannan muna fatan alkhairi ga mai martaba tsawon zaman sa anan jihar”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here