Osinbajo Yayi Bayani Kan Batun Neman Takarar Shugaban Kasa a Zaben Shekarar 2023

0
196

Kamar yadda ake ta batu na bawa yankin kudancin kasarnan dama a zaben shekarar 2023, Mataimakin shugaban kasa na daya daga cikin wadanda ake ganin zasu gaji shugaban kasa Buhari.

Sai dai, yayin da yake amsa tambaya a taron kungiyar lauyoyi ta kasa a yau Alhamis, Osinbajo yace niyyar sa a yanzu shine magance matsalolin dake bukatar dubawa.

“Akwai batutuwa dake bukatar a magance su wannan shine burina”.

A batun yawan kashe-kashe da ake samu a kudancin Kaduna, Osinbajo yace duk da matsalolin tsaro da kasarnan ke fuskanta, gwammati na samun nasara.

“Na shiga batun sasanta rikici a Kudancin Kaduna tun a shekarar 2001 ta hanyar kungiyoyin da ba na gwammati ba” inji shi.

“Da farko, mun bunkasa samar da tsaro a jihar Kaduna. Muna da sansanin sojoji yanzu haka, muna da jiragen yaki da tawagar jami’an soji wadanda zasu kula tare da tsare duk wani rikici a wajen.

” Shugaban kasa ya gudanar da taron tsaro wadanda dukkan su na halarta kuma an tattauna batutuwan.

“Sannan na zauna da shugabbanin al’umma a kudancin Kaduna, sannan mun zanta da Gwamnan jihar don lalubu matakan da za’a dauka na samun zaman lafiya”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here