Dattawan Kano Sun Soki Yunkurin Ganduje na Ciyo bashi Don yin aikin Layin Dogo

0
178

Gamayyar kungiyoyin hadin kan Kano ta Kano Unity Forum a yau Alhamis tayi suka ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa kudurin sa na ciyo bashin Kudi Biliyan 828 don yin aikin layin dogo a jihar Kano.

Kano Unity Forum gamayyar kungiyoyi sama da 15 ne dake a Kano.

A wata sanarwa da gamayyar kungiyoyin suka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS a yau Alhamis, kungiyar ta bayyana cewa Ganduje na neman ciyo bashin daga Bankin kasar China domin gudanar da aikin layin dogo a kwaryar birnin Kano.

Sanarwar dake dauke da sa hannun, Alhaji Bashir Usman Tofa tayi zargin cewa bashin ba ayi cikakken bayani akan sa ba kuma babu alamun gaskiya a ciki Sannan ba wanda yasan sharudan da aka cimma domin bayar da bashin”.

Kungiyar ta nemi cikakken bayani akan yarjejeniyar bayar da bashin inda tace “a matsayin mu na yan kasa zamu yi amfani da dokar bada bayanai kan wannan dalilin”.

Sannan sun yi barzanar daukar matakin shari’a kan Gwamna Ganduje kan dakatar da aikin layin dogon wanda suka bayynna shi a matsayin abinda al’ummar Kano basa bukata.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito kungiyar na neman Ganduje ya samar da kayan sawa na yan makaranta kala biyu zuwa uku ga daliban Firamare dake Kano wanda hakan zai ci kudi sama da Miliyan 3, sannan da samar da kayayyakin aiki ga asibitoci da sauran abubuwan cigaba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here