Adesina Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Bankin Raya tattalin Arzikin Afrika

0
161

Shugabannin hukumar gudanarwar Bankin raya tattalin arzikin Afrika sun sake zaben Akinwumi Adesina a matsayin shugaban Bankin.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Lauretta Onochie ce ta tabbatar da labarin a wani sakon taya murna data wallafa a shafinta na Twitter.

Babbakin raya tattalin arzikin Afrikan yanzu haka na gudanar da taron sa na shekara karo na 55 a Côte di’ivoire a kafar sadarwa.

Sake zaben Adesina yazo ne cikin rudani bayan an zarge shi da saba ka’idar aiki a kwanakin baya.

Sai dai, bayan gudanar da bincike, an wanke tsohon ministan noman na Najeriya daga zarge-zargen da aka yi masa wanda ya bashi damar koma karagar sa.

Adesina shine dan Najeriya na farko da ya rike shugaban Bankin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here