A Yau Ganduje Zai Sanya Hannu Domin Kashe Wanda yayi Batanci ga FIYAYYEN HALITTA

0
229

Wasu bayanai na nuni da cewa a yau Alhamis Gwamanan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai sanya hannu kan hukuncin da kotu ta yanke na kashe mawakin nan, Yahaya Aminu wanda yayi batanci ga ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

Wata majiya ta shaidawa jaridar PRIME TIME NEWS cewa gwamnan wanda ya dawo daga tafiya a ranar Litinin ana saran zai sanya hannu wanda zai bada dama wajen kashe mawakin kamar yadda kungiyoyi da dama suka nema.

Idan za’a iya tunawa dai Yahaya Aminu mai shekaru 22 kotu ta same shi da laifin batanci ga ANNABI MUHAMMADU S.A.W a watan Maris.

Karin bayani na nan tafe….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here