Yau Take Ranar Harshen Hausa Ta Duniya

0
171

 

A ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ce ake gudanar da bikin Ranar Hausa ta duniya.

Shekaru shida da suka gabata ne wasu fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta a ƙasar nan suka kirkiro da wannan ranar tare da kebe kowace ranar 26 ga watan Agusta a zaman ranar wannan bikin.

Da wuya a iya tantancewa, fayyacewa ko kuma sahihance asalin harshen Hausa da lokaci ko jinsi da al’ummar da suka fara yin amfani da shi. Sai dai kuma hakan bai hana manazarta, masana, masu bincike da kuma manyan malamai rika yin kirdado da kintacen kokarin gano asalin Hausa ba.

Harshen Hausa na daya daga cikin harsunan da ke yado, ba a nan Najeriya kadai ba, har ma a cikin kasashen Afrika ta Yamma da wasu kasashe da dama.

Ta ko wane fanni za a iya cewa Hausa ta samu karbuwa a duniya, idan aka yi la’akari da hanyoyin zamani na isar da sakonni, ilmantarwa da fadakarwa.

Harshen Hausa ya rika tumbatsa tare da samun karbuwa, idan aka yi la’akari da yadda Turawan mulkin mallaka suka rika amfani da shi wajen isar da sakonni da kuma mu’amala. Misali a zamanin Yakin Duniya na Farko, an rika amfani da harshen Hausa wajen isar da sakonni da mu’amala tsakanin sojojin da aka kwasa daga nan Arewa.

Ko a can baya, lokacin da Turawa suka shigo da kuma kafin zuwan Turawa, cinikayya da masu yawon fatauci daga kasar Hausa zuwa cikin wasu kasashe, sun taimaka wajen tumbatsar harshen Hausa a sassa daban-daban na Afrika.

Masana da manazarta da dama sun yi makaloli dangane da Harshen Hausa. Ko ma dai me kenan, hanyar sadarwa musamman kafar yada labarai ta kara haifar da tumbatsar harshen Hausa a duniya.

Tun ma kafin shigowar radiyo ko kuma yawaitar sa a Arewacin Najeriya, jarida na daya daga cikin kafar da ta taimaka wajen yada harshen Hausa da kuma samar da karbuwar sa a sassa daban-daban.

An fara buga jaridar Hausa ta farko, wato GASKIYA TA FI KWABO a cikin 1938. Wannan kuma tabbas ya na nuna cewa tun a lokacin Harshen Hausa ya shiga gaban sauran harsunan Najeriya kenan.

Shigar da Harshen Hausa a kafafen yada labarai na kasashen Turai, Amurka da wasu kasashe na cikin wasu Nahiyoyi, ya nuna karfin sa da kuma irin yadda ya ke da tasiri ga isar da sako da ilmantarwa.

An bude Shashen Hausa na Radiyon BBC London, VOA, Jamus, Faransa, China, Iran da sauran kasashe da dama. Kusan kasashen Afrika ta Yamma babu inda ba a magana da harshen Hausa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here