Wata Kotu ta dakatar da Manyan Motocin ‘Luxurious’ aiki a Kano

0
132

Wata kotu, dake zamanta a gidan Murtala, dake Kano karkashin jagorancin mai shari’a Rakiya Lami Sani a yau Laraba ta dakatar da masu manyan motoci na Luxurios gudanar da ayyukan su a jihar Kano.

Yanke hukunci yazo ne bayan kotun ta saurari bukatar lauyan gwamnati Mutawakkil Muhammad,  da kuma na ma’aikatar shari’a ta jihar Kano kuma mai baiwa hukumar KAROTA shawara kan fannin shari’a wanda ya nemi kotun ta dakatar da ayyukan manyan motoci a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa daukar matakin shari’ar yazo ne bayan da masu manyan motocin suka ki bin umarnin hukumar KAROTA na komawa filin ajiye motoci na unguwa uku.

Yayin da yake bayyana ra’ayin sa kan hukuncin kotun, shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi, ya gargadin cewa dukkan mai motar da yaki bin umarnin kotun zai fuskanci hukunci.

Sannan yace, duk da masu manyan motocin basu nemi damar gudanar da ayyukan su a Kano ba amma hukumar ta basu damar komawa sabon wajen ajiye motoci domin cigaba da kasuwancin su, amma duk da haka suka ki bin umarnin hukumar wanda ya jawo daukar matakin shari’a.

Ya bukaci wanda lamarin ya shafa da su bi umarnin kotun domin samun zaman lafiya da bin tsarin doka a Kano kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar KAROTO, Nabilusi Abubakar ya fitar a yau Laraba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here