Sarkin Karaye Ya Nemi Gwamnatin Jihar Kano ta Gina Gadar Sama a Masarautar Karaye

0
144

Gwammatin jihar Kano zata gina hanyoyin zamani da sanya fitilu a garin karaye dake masarautar Karaye.

Kwamishinan ayyuka kuma shugaban kwamitin ayyuka da tsare-tsare na masarautar, Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar fadar Sarki Sulaiman Ndoji.

Alhaji Idris Garba yace za’a tura tawagar kwararru yankin domin duba hanyoyin da suke bukatar a zamanantar dasu.

Kwamishinan yakara da cewa tawagar zata hada kai da masarautar karaye wajen gano hanyoyin.

Idris Unguwar Rimi ya tabbatar da cewa dukkanin masarautu biyar na jihar za’a kawata su yadda zasu yi gogayya da kowanne irin birni a kasarnan.

Kwamishinan ya kuma sanar da cewa aikin titin garin Kankare zuwa Kabo zai kammalu a shekarar 2021.

Sannan ya jinjinawa Sarkin Karaye tare da masarautar bisa goyon bayan da suke bawa gwamnatin jihar Kano wajen cigaban masarautar.

Yayin da yake mayar da martani, Sarkin na Karaye, Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II ya bayyana cewa aikin titin Kankar zuwa Kabo a matsayin babban cigaba a masrautar Karaye.

Sannan Sarkin ya nemi gwamnatin jihar ta gina gadar sama a masarautar ta Karaye.

Yayin da yake jawabin sa shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Alhaji Garba Shu’aibu ya bukaci gwamnatin jihar ta amince da fitar da kudi don gina masaukin gwamna a masarautar ta Karaye.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here