Rasuwar Hussein Hamed Mutumin da ya ƙirƙiro Bankin Musulunci babban giɓi ne

0
253

 

Allah ya yi wa ɗaya daga cikin mutanen da suka fara gudanar da tsarin banki da harkokin kuɗi na musulunci, wanda kuma ake ganin shi ne jagora a tsarin, Dakta Hussein Hamed, rasuwa a ranar Talata, 19 ga Agusta, 2020, in ji rahoton jaridar The Cognate.

Dakta Hussein ya kasance ɗaya daga cikin masanan da suka yi fice a duniya wajen aiwatar da mu’amalar kuɗi bisa tsarin shari’ar musulunci. Ya kasance mai bayar da shawara kuma memba na hukumomin mu’amalar kuɗi sama da ashirin a faɗin duniya, sa’annan kuma shine ya kasance kan gaba wajen kafawa tare da yin jagoranci a tsarin mu’amalar kuɗi na musulunci a gida da kuma ƙasashen waje. Ya shugabanci Kwamitin Bada Shawarwari kan Shari’a a bankunan musulunci da dama a yankin Gabas ta Tsakiya tare da bayar da shawara ga gwamnatocin ƙasashe da dama.

Dakta Hussein ya sami digirinsa na uku ne daga Tsangayar Ilimin Sharia ta Jami’ar Azhar da ke Alƙahira a shekarar 1965 sannan kuma ya sami digirin girmamawa daga Jami’ar Durham da ke ƙasar Birtaniya a cikin 2013. Ya kuma sami digiri na biyu a fannin Nazarin Nau’ukan Shari’o’i a Jami’ar New York da kuma digirin farko a fannin Shari’ar Zamani da ta Musulunci daga Jami’ar Alƙahira da Azhar.

A fannin aiki kuma, wanda ya shafe sama da shekaru 50 yana yi, Dakta Hussein ya kasance farfesa a fannin Shari’a a Jami’ar Alƙahira; shugaban Sashen Ilimi Mai Zurfi a Jami’ar Mohammed bin Ali Al-Sunusi da ke ƙasar Libya; shugaban Jami’ar Musulunci ta Ƙasa da ƙasa da ke Islamabad; mai bayar da shawara kan harkokin ilimin musulunci da aiwatar da sharia, Islamabad; mai bayar da shawara ga shugaban ƙasar Kazakhstan kan sharia da tsarin mulki; da kuma daraktan Hukumar Binciken Kimiyya da Farfaɗo da Al’adun Musulunci da ke birnin Makkah.

Haka kuma Dakta Hussein ya kasance memba na Majalisar Fatwa ta Ƙasashen Turai, wadda ƙungiyar ƙasa da ƙasa ce ta musulmi. Ya kuma taimaka wajen fassarar Alƙur’ani Mai tsarki zuwa harshen ƙasar Rasha tare da wasu littattafan musulunci guda 200 zuwa harsuna daban-daban.

Shi da kansa ya wallafa littattafai 21 da kuma maƙaloli sama da 400 sannan ya jagoranci gudanar tarukan karawa juna sani kan mu’amalar kuɗi a musulunci a sassa daban daban na duniya.

A lokacin rasuwarsa shi ne shugaban Majalisar Masana Shari’ar Musulunci ta Amurka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here