Messi Ya Kauracewa Atisayen Kungiyar Kwallon Kafa ta Bercelona

0
133

Lionel Messi ya shaidawa masu horar da kungiyar kwallon kafa ta Bercelona cewa bazai samu zuwa atisaye ba a ranar Laraba, kamar yadda sabon daraktan kungiyar Ramon Planes ya fada.

A ranar Talata ne dai Messi ya fadawa kungiyar cewa zai barta wacce ya kasance a ciki tsawon kakar wasanni 20.

“Messi ya fada mana cewa bazai samu damar zuwa atisaye ba”, cewar Planea yayin kaddamar da dan wasan Portugal Joao Trincao.

“Amma za’a cigaba da tattaunawa tsakanin dan wasan da kuma kungiyar”.

Planes dai ya gaji Eric Abidal ne wanda aka kungiyar ta kora bayan tasha kashi a hannun Bayern Munich da ci 8 da 2 wanda ya bar Kungiyar A matsayin wacce bata dauki ko wanne kofi ba a wannan kakar

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here