Wasanni: Messi Ya Nemi Barin Kungiyar Kwallon Kafa ta Bercelona Nan take

0
153

Shahararren dan wasan nan na kungiyar Kwallon kafa ta Bercelona, Lionel Messi ya fadawa kungiyar kwallon kafar ta Bercelona yana son barin kungiyar.

Kungiyar ta tabbatar da cewa dan wasan dan asalin kasar Agentina ya aiko mata da wani rubutu wanda aciki ya bayyana bukatar sa ta barin kungiyar.

Sanarwar na zuwa ne kwanaki 11 bayan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta lallasa Bercelona da ci 8 da 2 a wasan kusa da na karshe na gasar zakarun nahiyar turai, wanda shine rashin nasara mafi muni ga kungiyar kwallon kafa ta Bercelona a tarihi.

Messi ya samu nasarar lashe gasar fitaccen dan wasa ta Ballon D’or har karo 6 tsawon zaman sa a kungiyar kwallon kafa ta Bercelona, sannan ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofin Laliga har guda 10 da kofin zakarun nahiyar turai guda 4.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here