Wani Magidanci Ya Rasa Ransa a Kano Bayan Yunkurin Ceto Tinkiyarsa da ta Fada Rijiya

0
171

Abdulhamid Muhammad mai shekaru 55, Mazaunin garin Shaiskawa dake karamar hukumar Dambatta a jihar Kano ya rasa ran sa bayan yayin kokarin ceton tinkiyarsa da ta fada rijiya.

Mai magana da yawun hukumar kashe gabora ta Kano, Mr Saidu Muhammad ya tabbatarwa da jaridar PRIME TIME NEWS faruwar lamarin yau Talata a Kano.

Mista Saidu yace mamacin an ceto shi tare da kaishi asibitin garin Dambatta inda aka tabbatar da rasuwar sa.

“Bayan samun labarin, mun tura tawagar mu wadanda suka gano cewa dan shekara 55 ne mai suna Abdulhamid Muhammad wanda ya fada rijiyar.

Inda ya kara da cewa tashar kashe gobara ta garin Dambatta ya samu kiran waya da karfe 4:37 na asuba daga wata mai suna Ummi Muhammad a kauyen Sha’iskawa wacce ta fadawa hukumar abinda ya faru.

” Lamarin ya faru ne yayin da yake kokarin ceto akuyar sa wacce ta fada rijiya, bayan mun ceto mutum sai muka kaishi asibitin inda likita ya tabbatar da mutuwar sa”.

Malam Saidu ya kuma shawarci mutane da su dinga sanarwa hukumar kashe gobara irin wadandan abubuwan idan sun faru don dakatar da fadawar su cikin matsala.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here