Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta Nemi a Gina karamar Sakandire a wani yanki a jihar

0
114

Majalisar dokokin jihar Sokoto, a yau Talata ta amince da kudurin yin kira ga gwamnatin jihar don samar da karamar Sakandire a rukunin gidaje 500, dake tsohon filin tashi da saukar jirage a Sokoto.

Amincewar tazo ne biyo bayan kudurin da dan majalisar jiha mai wakiltar Sokoto ta guda, Alhaji Mustapha Abdullahi na jami’iyyar APC yayi, wanda kuma ya samu goyan bayan, Alhaji Habibu Modachi na jami’iyyar PDP.

Abdullahi yace kudurin ya zama dole la’akari da yawan jama’a dake karuwa a yankin, sannan kuma babu karamar Sakandire ko daya a yankin.

“Haka kuma, kafa makarantar a yankin zai taimaka matuka sosai wajen bunkasa ilimi sannann zai rage matsalolin zirga-zirga tare kuma da magance matsalar rashin zuwa makaranta a yankin.

” Kari kan haka, yunkurin wani bangare ne na shirin wannan gwamnatin na bunkasa ilimi”. Inji shi.

Kakakin majalisar, Alhaji Aminu Achida, ya nemi jin ra’ayin yan majalisar kan kudurin, wanda kuma take suka amince dashi.

A wani cogaban kuma, wata doka da aka gabatar a majalisar domin hana nuna wariya ga nakasassu, ta tsallake karatu na biyu a majalisar.

Cigaban yazo ne bayan kudurin da dan majalisa Alhaji Maidawa Kajiji, na jami’iyyar APC ya gabatar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here