Kwana Guda Bayan Ziyarar Sarki Sanusi, Sarkin Musulmai Ya Ziyarci El-Rufai

0
220

Mai alfarmar Sarkin Musulmai, Saad Abubkar, a yau Litinin ya kai ziyara ta musamman ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.

Ziyarar Sarkin Musulman na zuwa ne awanni 24 bayan ziyarar tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ga El-Rufai don tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da harkokin tattalin arzikin jihar.

Shigar sa ke da wuya gidan gwamnatin jihar, Sarkin Musulmai ya wuce ofishin gwamnan jihar inda ya shiga tattaunawar sirri da El-Rufai tare wasu jami’an gwamnatin jihar da suka hada da Sanata mai wakiltar Arewacin Kaduna, Sulaiman Abdu Kwari.

Sai dai, Sarkin Musulman yaki amincewa yayi magana da yan jarida bayan tattaunawar, amma Nasiru El-Rufai yace an tattauna matsalar tsaro a yankin kudancin Kaduna da sauran bangarorin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa ya karbi shawarwari da kalaman karfafa gwiwa daga Sarkin da zasu taimaka wajen kawo mafita ga matsalar tsaro a jihar.

Ya godewa Sarkin Musulman bisa ziyarar da kuma goyan baya domin tabbatar da ingantuwar tsaro a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here