Kwamishinan Lafiya Ya Kamu da Cutar COVID-19

0
190

Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya kamu da cutar Coronavirus.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Gbenga Omotoso ne ya sanar da hakan a yau Litinin a shafin sa na twitter.

Inda yace, “Saboda yawan kusanci da mutanen da suke jin rashin lafiya kuma akayi musu gwaji ya tabbatar suna da cutar, kwamishinan lafiya, Farfesa Akin Abayomi, gwaji ya nuna yana dauke da cutar COVID-19, Abayomi ya tabbatar da kamuwa da cutar ne bayan da tsarin yin gwajin cutar ga wadanda suka yi mu’ammala da masu dauke da cutar.

“Haka kuma, yana cikin koshin lafiya ba tare da nuna alamun cutar ba”.

“Kwamishinan lafiyan zai cigaba da killace kan sa a gida har tsawon kwanaki 14.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here