Gwamnatin Jihar Kano ta Amince da Biyan Kudin Jarrabawar NECO Ga Dalibai 29, 126 Yan Asalin Jihar Kano

0
334

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe kudi N489, 258 don biyan kudin yin rijistar jarrabawar kammala Sakandire ga dalibai 29, 126 yan asalin jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta amince da sakin sakamakon jarrabawar tantancewa ta Qualifying.

Amincewar tazo ne dai-dai lokacin da ake shirye-shiryen yin jarrabawar kammala Sakandire, yayin da daliban da gwamnatin ta dau nauyi zasu zana jarrabawa NECO da NBAIS.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta Kano, Ali Yusif ya fitar jiya tace, amincewar tazo ne bayan kwamishinan ilimi, Muhamamad Sanusi Sa’idu Kiru ya gabatar da bukatar hakan ga majalisar zartarwar jihar.

La’akari da bukatu uku daga da kwamishinan ya gabatar ga majalisar zartarwar, gwamnatin jihar tayi la’akari da zabi na uku na daukar nauyin daliban.

“Acikin wannan tsarin, gwamnatin jiha zata dau nauyin dalibai 29, 126 da suka sami Credit 5 zuwa sama wadanda suka hada da English da Math a jarrabawar Qualifying”.

Sanarwar ta kara da cewa” yayin da yake taya murna ga daliban bisa kwazon da suka nuna, kwamishinan ya bukace su su tabbata sun samu nasarar jarrabawar NECO da NBAIS.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here