Dole ne ayi Gwajin Cutar Corona Ga Masu Son Shigowa Najeriya daga Kasashen Ketare -FAAN

0
147

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa(FAAN) tace Fasinjoji masu son zuwa Najeriya yayin da aka dawo da zirga-zirgar jiragen kasashen ketare dole ne ayi musu gwajin cutar COVID-19 makwo biyu kafin zuwan su.

Musa Shu’aibu Nuhu, Babban Darakta a hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ne ya sanar da hakan a makon da ya gabata yayin jawabi na kullum da kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 a Abuja. Inda ya kara da cewa dukkan masu son barin kasarnan suma sai sun nuna sakamakon gwajin cutar COVID-19 da ya nuna basa dauke da cutar, sannan za’a bar su su hau jirgi.

A wani sako da hukumar FAAN ta wallafa a shafin ta na Twitter tace gwajin dole na cutar COVID-19 yana daga cikin bangare na matakan da aka tsara na sake dawo da jigilar jiragen kasashen ketare.

Gwamnatin tarayya dai ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasashen ketare a ranar 23 ga watan Maris sakamakon barkewar cutar COVID-19.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here