Babu Wani Shiri na Sanyawa Mutanen Kano Haraji – Ganduje

0
146

A kokarin sa na kawo karshen annobar COVID-19 a jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da bayar da kayan tallafi ga masu biyan haraji da kamfanunuwa domin taimakawa musu wajen farfado da harkokin kasuwancin su.

Shugaban hukumar tattara haraji ta Kano, Abdul-Razak Datti Salihi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da jaridar PRIME TIME NEWS yau Litinin jim kadan bayan taron bada horo na kwana guda a Kano.”Gwamna ya bada umarnin fitar da kayan tallafi don bawa masu biyan haraji damar gudanar da harkokin kasuwancin su da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Hukumar tattara haraji ta Kano ce dai ta shirya taron bada horon.

Mr Salihi ya nemi yan kasuwar jihar Kano da su dinga biyan haraji akai-akai inda yace gwamnati baza ta sanya abin da zai matsaya yan gari ba wanda zai sa kamfanunuwa su durkushe.

“Gwamnatin Ganduje a koyaushe tana tsaye wajen samar da tsaro da ayyukan cigaba ga mazauna Kano. Hakan zai faru ne ta hanyar biyan haraji”.

Sannan yayi barazanar cewa gwamnatin jihar Kano zata hukunta yan kasuwar da suka gaza biyan haraji.

Haka kuma ya bukaci yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a jihar su fadakar da mutane kan alfanun manufar Ganduje na inganta tattalin arzikin Kano.

A yayin da yake nasa jawabin, mai taimakawa gwamnan Kano kan sha’anin tattara haraji, Habib Sale Muhammad Mai-Lemu ya yabawa Ganduje bisa amince da raba kayan tallafin ga yan kasuwa a jihar.

Mai -Lemo yace manufar shirin shine rage radadin annobar a Kano tare da bada dama wajen gudanar da kasuwanci cikin wal-wala.

Da yake bayyana ra’ayin sa kan jita-jitar cewa Ganduje na shirin sanya sabon haraji ga mutanen Kano, Mai Lemo ya musanta batun inda yace ” Babu wani shiri na sanyawa yan Kano haraji, kuma hakan bazai taba faruwa ba”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here