Ba’a Sanya Ranar Sake Bude Makarantu Ba -Gwamnatin Tarayya

0
728

Gwamnatin tarayya a yau Litinin tace babu wata rana da aka sanya za’a sake bude makarantu duk da ana cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don duba yadda za’a koma makarantun.

Karamin ministan Ilimi, Mr Chukuwemeka Nwajiuba ne yayi bayanin haka a jawabin kullum-Kullum da kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da annobar COVID-19 keyi a Abuja.

Sannan ya bukaci daliban manyan makarantu wadanda suke korafin cigaba da rufe makarantun su kara hakuri da gwamnati.

Ministan ya bayyana cewa ranar da za’a dawo makarantun na nan zuwa.

Hakanan ya kara da cewa shi da babban ministan ilimi Adamu Adamu, sun zauna da masu ruwa da tsaki na manyan makarantu akan batun.

Inda yace jami’o’i 78 wanda yawancin su masu zaman kansu ne sun bayyana cewa sun shirya komawa cigaba da karatu yayin da jami’i’on gwamnati kashi hamsin su ne suka mayar da martani

Sannan ya tabbatar da cewa bayan tattara ra’ayoyi, zai gabatar dasu ga kwamitin fadar shugaban kasar domin dubawa kafin sanar da ranar komawa makarantun.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here