An Hana Masu Ababan Hawa Amfani da Wayar Hannu a Gidajen Mai

0
113

Sashin kula da albarkatun mai na kasa DPR ya hana masu motoci yin amfani da wayar salula yayin da suke siyan mai a gidajen mai domin hana barkewar gobara.

Oulusegun Dabo, babban mai kula da ayyukan sashin a jihar Osun, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) cewa amfani da wayoyin salula a gidajen mai akwai hatsari mai girma.

Sannan Mr Daboh ya bukaci masu motocin su dinga kashe motar su kafin su zuba mai.

Haka kuma yayi gargadin cewa yan kasuwar dake tafikar da gidajen mai ba bisa ka’ida ba da wadanda damar ayyukan su suka kare zasu fuskanci dakatarwa.

Yace dukkan wasu abubuwa da suka sabawa doka da yan kasuwar mai suke yi za’a dau mataki akai da zarar an sanarwa da ofishin DPR din.

Daboh ya kara da cewa kwamitin kar ta kwana na sashin kula da albarkatun mai na kasa zai cigaba da zagayawa gidajen mai don tabbatar da ana bin ka’idojin da aka shimfida.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here