Shin Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II Zai Dawo Sarautar Kano?.

0
1192

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya sauka a jihar Kaduna a Safiyar yau Lahadi da Misalin karfe 10:30, inda ya samu tarbar manyan jami’an gwammatin jihar da sarkin Saminaka.

Hakanan daruruwan magoya bayan tsohon sarkin ne suka yi dafi-fi wajen tarbar sa wanda ya taso daga brinin Legas zuwa jihar Kaduna domin saukakawa masu kaimasa ziyara.

Jim kadan bayan saukar Sanusi a jihar ne, dashi da tawagar sa ya wuce zuwa gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda dubban masoyan tsohon sarkin suka dinga mika kaisuwa a gare shi.

Sanusi dai shine sarki na 14 a masarautar Kano, kafin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya cire shi daga mukamin sa bisa zargin rashin biyayya ga gwamnati.

Sai dai, yayin da daruruwan magoya bayan tsohon Sarkin ke tarbar sa a jihar Kaduna anjiyo su suna ta addu’ar”Allah ya dawo da Sarkin Turakar Dabo”.

Yayin da wasu masana shari’a ke ganin an tube Sanusi ba bisa ka’ida ba, amma yace bazai kalubalanci tube shin a gaban kotu ba.

Wasu dai na ganin cewa har yanzu Sanusi II nada sha’awar komawa sarautar Kano, ganin yadda yake shiga irin ta Sarki da zaman fadanci a gidan sa dake Birnin Legas.

Za’a iya cewa zaben shekarar 2023 ne kadai zai yanke hukunci kan yuwuwar dawowar Sanusi Karagar mulkin Kano, Matuakar Yan adawa suka samu nasarar lasheshi ko kuma jami’iyyar dake mulki ta kara samun nasara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here