‘Sauraron Wakokin Marigayi Lil-Ameer ne Yaja Hankalina Wajen Fara wakar Hip-Pop’ -Abba Talantino

0
339

Matashin mawakin gambara na Hausa Hip-Pop, Abba Sani Jakada wanda ake kira da Talantino yace sauraran wakokin Lil-Ameer, DJ AB da Sauran Mawakan Hip-Pop ne yaja hankalin sa wajen fara yin waka.

Mawakin wanda yake dan Asalin unguwar Gama ne dake karamar hukumar Nasarawa a Kano ya bayyana hakanne yayin tattaunawa da jaridar PRIME TIME NEWS a jiya Asabar.

“Na tsinci Kaina a harkar waka ne yayin da nake yawan sauraron wakokin Hip-pop irin na su DJ AB, Musamman ma yaron nan da ake cemasa Lil-Ameer”. Inji mawakin.

Mawakin yace bai taba tunanin zai fara waka a rayuwar sa ba, amma a sannu a hankali sai gashi ya fara waka.

Haka kuma mawakin yace yafi kaunar wakar Pick-Up cikin wakokin nasa, sanna yace yana shirin fitar da wata sabuwar waka wacce zai yi featuring dan gidan Shaba.

Abba Sani Jakada, yace ya fuskanci kalubale da dama” na fuskanci kalubale da yawa wani zubin nayi ace bai yi dadi wani zubin ace yayi dadi”.

Mawakin yace ya samu nasarori da dama a fannin waka, sannan yayi godiya ga masoyan sa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here