Sanusi Ya Soki Kungiyar Lauyoyi ta Kasa Bisa Janye Gayyatar da tayiwa El-Rufai

0
205

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soki shawarar da kungiyar lauyoyi ta kasa ta yanke na janye gayyatar da tayiwa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai zuwa halartar taron ta na kasa. Inda ya bayyana matakin janye gayyatar da abin bacin rai ga yancin yin magana a Najeriya.

Sanusi na magana ne a yau Lahadi yayin ziyara zuwa jihar Kaduna, ziyarar sa ta farko zuwa Arewacin Najeriya tun bayan cire shi daga sarautar Kano a farkon wannan shekarar.

Kungiyar lauyoyi ta kasa dai ta gayyaci El-Rufai yayi bayani a taron ta na shekara sai dai ta janye gayyatar a makon da ya gabata bayan wasu tsagi a kungiyar sun yi suka ga gayyatar gwamnan wanda suka ce ya gaza wajen shawo kan matsalar tsaro a yankin kudancin Kaduna.

Yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar, Sarki Sanusi yace yana sane da cewa yawancin mambobin kungiyar basa farin ciki da matakin hana gwamna yin bayanai yayin taron.

“Ina sane da cewa dayawan lauyoyi basu amince da wadandan nan zarge-zarge ba. Kasan idan kana da ra’ayi, mutane ko dai su yarda da kai ko suki yarda da ra’ayin ka. Amma mutumin da yake da ra’ayi wanda za’a iya aminta ko kin aminta dashi a kodayaushe yafi wanda bashi da ra’ayi a komai. Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here